Muhallinka Rayuwarka RFI Hausa
-
- News
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).
-
A duk shekara Nijar na asarar Eka ko kadadar noma dubu dari sakamakon zaizayewar Ƙasa
‘Muhallinka Rayuwarka’ shiri ne da zai leka Jamhuriyar Nijar, inda wani rahoton ma’aikatar kididdiga ke cewa a duk shekara kasar na asarar Eka ko kadadar noma dubu dari sakamakon zaizayewar Ƙasa da gusowar hamada. Lamarin da ya zama babban koma baya ga ayyukan wadata kasa abinci. Wata matsalar ita ce ta sallacewar kasa da komawarta hako da ba a iya noma a kai.
-
Nigeria daya daga cikin kasashe masu noman auguda a nahiyar Afrika da duniya
Shirin a wannan mako zai ba da hankali ne akan noman auduga,
a shekarun baya, Nigeria ta kasance daya daga cikin kasashe masu tinkaho da noman auguda a nahiyar Afrika da duniya baki daya.
Sai dai hankalin mahukuntan kasar ya koma ga bangaren man petur bayanda Allah ya albarkaci kasar da mai.
Jihohin da suka yi fice a noman auduga a kasar, sun hada da Zamfara, Katsina, Kano, Adamawa, Bauchi da kuma Gombe. -
Matsalar yoyon iskar gas yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha yankin Delta
Shirin na wannan mako zai yi dubi ne akan yadda al'ummar karamar hukumar Obagi na jihar RIVERS dake yankin NIGER DELTA tarayyar Najeriya suke fama da matsalar yoyon iskar gas sanadiyar fashewar bututun da aka samu tun a watan Yunin shekarar 2023 wanda yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha, wanda ya sa al'ummar ke kamuwa da cutar amai da gudawa har zuwa wannan lokaci.
-
Matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka don magance matsalar tsuntsaye a gonaki
Shirin 'Muhalli' na wannan makon tare da Nasiru Sani ya mayar da hankali ne kan tu’annatin da wasu nau'in tsuntsaye da ake kira jan-baki ke yi wa gonaki a Najeriya tare da kokarin da gwamnati ke yi domin shawo kan lamarin.
-
Yadda tsananin zafi ya ci karo da lokacin azumin watan Ramadana
Shirin a wannan mako zai ba da hankali ne akan tsananin zafin da ake fama da shi a wasu yankuna na Nahiyar Afirka, a wannan shekarar ya tsananta inda a wasu sassa na tarayyar Najeriya lamarin ya dan wuce misali.
Jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya, jiha ce da tun asali aka sani da tsanantar kowane juyin yanayi na Zafi ko na Sanyin Hunturu ko ma na yawan saukar Ruwan sama.
Sai a latsa alamar sauti domin sauraron shirin. -
Kaddamar da shirin inganta harkokin noma a jihar Niger
Shirin na wanna makon zai yi dubi ne akan katafaren shirin zamanantar da aikin noma da gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta kaddamar. Masana na ganin Jihar a matsayin wadda idan aka tattala kasar noma da take da ita, a cikinta kadai za a iya noma abincin da zai iya ciyar da kasar har ma a iya fitarwa zuwa kasashen ketare.