100 Folgen

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, al’adu da dai sauransu…

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare RFI - Radio France Internationale

  • Nachrichten

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, al’adu da dai sauransu…

  Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare - Ra'ayoyin masu sauraro kan shirin Majalisar Dattawan Amurka na wanke shugaba Trump

  Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare - Ra'ayoyin masu sauraro kan shirin Majalisar Dattawan Amurka na wanke shugaba Trump

  Shirin ra'ayoyin ku masu sauraro na wannan lokaci tare da Zainab Ibrahim, ya tattauna matakin Majalisar Dattawan Amurka na kada kuri’ar kin amincewa da matakin kiran masu bada shaida da kuma tattara sabbin hujjoji dangane da tsige shugaban kasar Donald Trump. Ana ganin matakin da Majalisar Dattawan mai rinjayen ‘yan Jam’iyar Republican ta dauka, zai kai ga wanke Trump daga zarge-zargen amfani da karfin ikonsa ta hanyar da ba ta dace ba.

  Tuni Majalisar Wakilan kasar ta tsige shugaban daga karagarsa.

  • 13 Min.
  Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare - Ra'ayoyin masu sauraro kan matakin kasashen yammacin Afrika dake mafani da kudin CFA

  Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare - Ra'ayoyin masu sauraro kan matakin kasashen yammacin Afrika dake mafani da kudin CFA

  Shirin ra'ayoyin masu saurare ya tattauna kan matakin kasashen yammacin Afrika 8 renon Faransa, da suka amince da sauya sunan takardar kudin da suke amfani da ita a hukumance daga CFA zuwa Eco, a daidai lokacin da kungiyar kasashen yammacin Africa ke shirin samar da kudin bai - daya mai suna ECO, lamarin da ake ganin riga – malam masallaci ne ga shirin na ECOWAS.

  • 15 Min.
  Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare - Ra'ayoyi kan tasirin dakarun kasashen ketare wajen yakar ta'addanci a Sahel

  Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare - Ra'ayoyi kan tasirin dakarun kasashen ketare wajen yakar ta'addanci a Sahel

  Taron shugabannin kasashe 5 na yankin Sahel da ya gudana ranar lahadi a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, ya jaddada muhimmancin ci gaba da hulda da kasashen duniya don yaki da ta’addancin a yankin na Sahel.

  Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da, a wasu kasashe aka fara nuna shakku dangane da irin rawar da dakarun kasashen yammacin duniya ke takawa a wannan yaki.

  Menene ra’ayoyinku game da amfani ko rashin amfani dakarun kasashen ketare a wannan yaki?

  Anya yankin Sahel zai iya tabbatar da tsaron kansa ba tare da gudunmuwar kasashen ketare ba?

  Kan wannan batu muka baku damar tattaunawa da musayar ra’ayoyi.

  • 14 Min.
  Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare - Ra'ayoyi kan kashe jami'an kungiyar agajin Faransa da Boko Haram tayi

  Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare - Ra'ayoyi kan kashe jami'an kungiyar agajin Faransa da Boko Haram tayi

  Kungiyar agajin kasar Faransa ta Action Against Hunger ta sanar da kashe jami’an ta guda 4 da kungiyar Boko Haram tayi garkuwa da su tun a watan Yuli.

  Kisan ya gamu da suka daga Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma kungiyar agajin dake taimakawa mutane 300,000 da rikicin Boko Haram ya tagayyara.

  Kan wannan batu muka baku damar tattaunawa a wannan litinin.

  • 15 Min.
  Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare - Ra'ayoyi kan batutuwa dake ciwa masu saurare tuwo a kwarya

  Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare - Ra'ayoyi kan batutuwa dake ciwa masu saurare tuwo a kwarya

  Shirin ra'ayoyin maso sauraro kowace Jumma'a na bada damar tofa albarkacin bakin kan duk wasu batutuwa da ke cimmuku tuwo a kwarya, a wannan karon ma masu saurararo sun bayyana ra'ayoyin su kan batutuwa da dama.

  • 15 Min.
  Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare - Ra'ayoyin Masu Saurare kan yawaitan harin ta'addanci a sansanonin sojin kasar Mali

  Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare - Ra'ayoyin Masu Saurare kan yawaitan harin ta'addanci a sansanonin sojin kasar Mali

  Shirin ra'ayoyin masu sauraro na wannan lokaci tare da Zainab Ibrahim,ya tattauna kan yawaitan hare-haren ta'addanci a sansanonin sojin kasar Mali, wanda ake ganin ya hallaka dakarun Mali sama da 100, duk kuma da cewa akawi dakarun G5 Sahel da na kasashen waje a kasar.

  • 15 Min.

Top‑Podcasts in Nachrichten

Mehr von RFI - Radio France Internationale