![](/assets/artwork/1x1-42817eea7ade52607a760cbee00d1495.gif)
24 episodes
![](/assets/artwork/1x1-42817eea7ade52607a760cbee00d1495.gif)
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare RFI Hausa
-
- News
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, al’adu da dai sauransu…
-
Ra'ayoyin masu saurare kan ɓarkewar cutar kwalara a Najeriya
Hukumar Yaƙi da Cututuka Masu Saurin Yaɗuwa a Najeriya, ta ce kawo yanzu adadin waɗanda suka kamu da cutar Amai da gudawa wato Cholera sun kai dubu 1 da 579, kuma tuni 54 daga cikinsu suka riga mu gidan gaskiya.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan ɓarkewar zanga-zanga a Kenya
Yunƙurin ƙara haraji a kan kayayyakin masarufi, ya haddasa ɓarkewar mummunar tarzoma a Kenya, inda aka tabbatar da mutuwar mutane da dama a jiya labara musamman a birnin Nairobi.
-
Mabanbantan ra'ayoyin masu saurare kan abubuwa da dama
RFI Hausa na bai wa masu saurare damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya a kowacce ranar Juma'a.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan matakin IPOB na shiga tattaunawa da Najeriya
Jagoran IPOB da ke fafutukar kafa ƙasar Biafra a Najeriya Nnamdi Kanu, ya ce a shirye yake ya shiga tattaunawa da gwamnati domin kawo ƙarshen kai-da-kawon da ake yi da shi a gaban kotu.
-
Ra'ayoyi kan rikici tsakanin Nijar da Benin
Rikici tsakanin Nijar da Jamhuriyar Benin, ga alama zai iya ɗaukar dogon lokaci kafin a iya warware shi, saboda ko bayan rufe iyaka, Nijar ta rufe bututun da ke isar da ɗanyan mai zuwa Cotonou.
-
Ra'ayoyi kan samar wa da Afrika alluran rigakafin cututtuka
Gabanin taron da za a gudanar ranar Alhamis a birnin Paris don taimaka wa Afirka dangane da yadda za ta samar wa kanta da alluran rigakafin kariya daga wasu cututuka a wadace, tuni aka samu alƙawurran sama da Euro biliyan ɗaya daga ƙasashe da da kuma ƙungiyoyi daban daban a cewar fadar gwamnatin Faransa.