Lafiya Jari ce RFI Hausa
-
- Science
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.
-
Har yanzu 'yan Najeriya da dama basa cin gajiyar shirin Inshorar lafiya -Bincike
Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba ne kan yadda har yanzu wasu daga cikin al’ummar Najeriya basa amfani da tsarin inshorar lafiya. A shekarar 2022 ne gwamnatin kasar ta sake dawo da dokar inshorar lafiya da aka samar tun 1999, a wani yunƙuri na sauƙaƙawa Jama’a samun kulawar lafiya cikin rahusa, lura da yadda kaso mai yawa na al’ummar ƙasar ke rasa kudaden iya kai kansu ga likitoci ko da suna cikin matsananciyar cuta.
-
Yara 'yan kasa da shekaru biyar na gaza samun alluran rigakafin da ta dace
Shirin na wannan mako ya duba yadda kananan yara musamman a Najeriya da sauran kasashe masu tasowa ke gaza karbar alluran rigakafin da ya kamata su samu kafin cika shekaru biyar da haihuwa.
-
Halin da ake ciki a yaki da cutar yunwa tsakanin kananan Yara a Jamhuriyar Nijar
A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya yi duba ne a kan halin da ake ciki a yaki da cutar Tamuwa tsakanin kananan Yara a Jamhuriyar Nijar.
-
Bayani a kan cutar ƙyanda da yadda za a kare yara daga kamuwa
A wannan makon shirin zai yi duba kan cutar kyanda ko kuma measles a turance, cutar da galibi akan ga bullarta a irin wannan lokaci da ake fama da matsanancin zafi musamman a yankunan kasashen yammacin Afrika Sahel.
-
Yadda matasa ke rungumar tsarin yin kaho a zamanance
Shirin lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan tsarin yin kaho a zamanance
-
Karancin ruwa na haddasa tarin cutuka ga al'ummar arewacin Kamaru
Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda al’ummar yankin arewacin kamaru ke fuskanta matsalar rashin tsaftatacce kuma wadataccen ruwan sha ba, wanda ke haddasa gagarumar matsala ga lafiyar mazauna yankunan, wannan shi ne maudu’in da shirin na wannan mako zai mayar da hankali akai.