Wasanni RFI Hausa
-
- Sport
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
-
Bitar yadda aka kammala kakar wasanni ta bana
Shirin a wannan mako shirin ya yi sharhi ne kan yadda aka kammala gasar La liga da wasan karshe na kofin FA da sauran abubuwan da suka faru a karshen wannan mako. Haka nan shirin ya yi tsokaci game da babban wasan da za a iya cewa ya rage a nahiyar Turai a wannan kaka wato wasan karshe na gasar Zakarun nahiyar da za ayi tsakanin Real Madrid da Borussia Dortmund.
-
Manchester City ta kafa tarihi bayan lashe kofin Firimiyar Ingila karo 4 a jere
Shirin duniyar wasanni na wannan mako ya yi duba ne a kan yadda aka kammala gasar Firimiyar Ingila, musamman yadda kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kafa sabon tarihin lashe gasar karo 4 a jere.
-
Har yanzu akwai rashin tabbas game samar da ingantaccen tsaro yayin gasar Olymics mai zuwa
Shirin duniyar wasanni na wannan mako ya dubi yadda ake tufka da warwarwa game da tsarin samar da cikakken tsaro yayin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci.
-
Nazari kan yadda wasannin kwata finals na gasar zakarun Turai su ka gudana
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda wasannin matakin kwata finals na gasar zakarun Turai su ka gudana. A makon da ya gabata ne dai aka kammala wasannin zagayen, inda aka fafata a wasanni 4. Dortmund da aris Saint-Germain da Bayern Munich da Real Madrid ne suka kaiga wasan kusa da na karshe a gasar ta bana.
-
Hasashen yadda za ta kaya a gasar Firimiyar Ingila
Shirin a wannan lokaci ya fi karkata akalar ne kan gasar Firimiyar Ingila, wadda ke ci gaba da jan hankali, duk da shawo gangarar da akayi.
-
Shiri na musamman kan shirye-shiryen gasar Olympics kashi na 2
A wannan makon Shirin Duniyar Wasanni ya yi duba ne kan yadda ake tufka da warwara game da tsarin tsaro a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci a watan Yulin wannan shekarar.