
79 episodes

Birbishin Rikici HumAngle
-
- News
Kokarin nutsawa cikin wahalhalun da mutanen da ke zaune a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula ke fuskanta, yawanci yakan zo ne kawai ta fuskar kididdiga; Birbishin Rikici wani shiri ne na mako-mako akan waɗannan labarun sirri na wadanda rikici da tashin hankali suka shafa da HumAngle ke kawo muku.
-
Ciwon Zama Dan Gudun Hijira A Inda Yaki Ya Wargaza
Tun lokacin da aka fara rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya, rayuka da yawa sunyi muni ga miliyoyin mutane. Yakura Kumshe na daya daga cikin wadannan mutanen.
Mun tambaye ta yadda take ji game da yadda al’amura suka sauya cikin sauri, tun daga ranar a Kumshe lokacin da ita da danginta suka san cewa dole ne su gudu zuwa Maiduguri. Tayi magana mei tsawo.
Marubuciya: Hauwa Shaffi Nuhu
Muryoyin Shiri: Khadija Gidado
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media -
Tun Da Aka Kama Mamio Ba A San Inda Yake Ba!
Shekaru goma da suka gabata, yayin da rikicin Boko Haram ya yi kamari a Maiduguri, harkokin kasuwanci sun koma baya. Don haka, Alhaji Modu ya yanke shawarar tafiya zuwa birnin Legas da ke kudancin Najeriya, tare da fatan sayar da amfanin gonan sa. Bayan shekara goma, har yanzu bai dawo ba.
Marubuci: Kunle Adebajo
Muryoyin shiri: Khadija Gidado
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media -
Komawa Gida Ko Sake Barinsa?
A shekarar 2021, gwamnatin jihar Borno ta sanar da cewa za ta rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Maiduguri tare da fara tsugunar da mutanen garin a garuruwansu ko wasu garuruwa.
Hakan dai ya kasance ne domin a rage yawan ‘yan gudun hijira a babban birnin kasar da kuma kara samun karfin gwiwa a tsakanin mutanen da suka dogara da kayayyakin agaji tsawon shekaru.
Marubuciya: Yakura Kumshe
Muryoyin shiri: Zubaida Baba Ibrahim
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: Ahmad Salkida -
'Ba Rai, Ba Mutuwa'
Ragowar kuɗaɗen ayyukan jin kai ga ƴan gudun hijirar da ba su da mafita yana janyo shigarsu tsakiyar hatsarin hare-hare da ke faruwa idan sun fita gonaki don neman samun kudin siyan abinci.
Daya daga cikin irin wadannan mutanen shine Hagola Biya, mahaifi ga yara 14 kuma mijin mata biyu.
Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Marubuci: Murtala Abdullahi
Muryoyin shiri: Akila Jibrin
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: Ahmad Salkida -
Rayuwa A Daular Boko Haram
Yaya rayuwa take a matsayin macen da aka sace a yankin Boko Haram? Yaya ya bambanta da rayuwa a cikin yankuna da ke ƙarƙashin ikon gwamnati?
Saurari labarin Amina a cikin shiri na wannan mako.
Mai gabatarwa: Rukayya Saeed
Marubuciya: Anthony Asemota
Muryoyin shiri: Khadija Gidado
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: Ahmad Salkida -
Ta Rasa Matsuguni, Ta Kamu Da Cuta
Mata a sansanin Malkohi da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya na fuskantar wani yanayi na musamman daga amfani da wuraren da ba su da tsafta a sansanin.
Cututtukan farji, kaikayi da suke kira ‘cutar bayi’ na shafar rayuwarsu.
Mai gabatarwa: Rukayya Saeed
Marubuciya: Zubaida Baba Ibrahim
Muryoyin shiri: Khadija Gidado, Zubaida Baba Ibrahim, Sabiqah Bello
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: Ahmad Salkida