
485 episodes

Najeriya a Yau Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim
-
- News
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
-
Abin Da Mutumin Da Ya Wuce Shekara 30 Ya Kamata Ya Yi
A Jiya Alhamis cikin shirin Najeriya A Yau mun dubi yadda da zarar an ga shekaru sun dan fara ja ana sa ran a cimma wani buri na rayuwa da zai sa a ga cewa mutum ya fara samun cigaba da zama cikakken mutum. Mun yi amfani da shekaru 30.
Shin ka saurari wannan shirin da ya yi magana kan Matakin Da Ya Kamata Matashi Ya Kai Kafin Ya Cika Shekara 30?
A yau shirin na tafe da shawarwarin mafita ga wadanda su ka wuce shekaru 30 amma babu kwakkarar madafa. -
Wane Mataki Ya Kamata Mutum Ya Kai Kafin Shekara 30
Shin kun taba tambayar kanku matsayin da ya kamata matashin da bai wuce shekara 30 ya taka?
Da zarar shekaru sun ja ana sa ran a cimma wani buri na rayuwa da zai sa a kalli cewa mutum ya fara samun cigaba da zama cikakken mutum.
Shirin Najeriya a Yau ya duba matakin da ya kamata a ce mutum ya kai kafin cika shekara talatin a rayuwa. -
Makomar Kakakin Majalisa Ɗan Jam'iyar Adawa A Filato
Ana ta kai ruwa rana a majalisar jihar Filato gameda yadda shugabanci zai kasance daga ɗan jam'iyar adawa da ba su da rinjaye.
Akwai 'yan majalisar APC da kotu ta baiwa nasara bayan tsige mafi yawancin yan jam'iyar PDP, duk da yake ba a rantsar da su ba amma majalisa tana hutu.
Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ake tirka-tirka a majalisar dokokin jihar Filato da zargin barazanar tsige kakakinta. -
Manyan Cututtukan Da Zazzabin 'Malariya' Ke Iya Janyowa
Jama’a na yi wa zazzabin malariya kallon wani zazzabi da bai taka kara ya karya ba. Sai dai kuma masana suna yiwa wannan zazzabi wani irin kallo.
Ko kun san manyan cutukan da zazzabin malariya zai iya haifarwa?
Shirin namu na wannan lokaci na tafe da gamsassun bayanai kan hanyoyin kariya. -
Yadda Ýan Damfara Ke Turawa Mutane “Rasit” Da “Alat” Din Bogi
Ýan damfara kullum na kara kaimu wurin fito da sabbin dabarun cutar jamaá ta hanyoyi daban daban.
Shin ko kun san ana iya tura maka alat da rasit din kudi na bogi?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da wadansu da aka turawa rasit da alat na bogi, ya kuma ji ta bakin wani masani kuma mai sharhi akan dabarun sadarwa ta intanet. -
Yadda Mabaratan Zamani Ke Neman Hana Bayar Da Sadaka
Lamarin ya kai da wuya mutum ya fito ya koma gida ba tare da wani ya yi masa ba-zata ya roke shi kudi ko abin ci ba.
Yawancin masu irin wannan rokon sukan fito ne tsaf-tsaf kamar wasu ma’aikata ko ’yan kasuwa.
Shin yaya jama’a ke kallon wannan dabi’a da ta zama ruwan dare?
Shirin Najeriya A Yau na wanna lokaci na tafe da karin bayani.