Shirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa a yau mayar da hankali kan rashin jituwar dake faruwa tsakanin gwamnoni a Najeriya da kuma ɓangaren Sarakunan gargajiya wanda har takai ga wasu jihohin na rushe Masarautu suna kuma kirkirar sababbi.
A ‘yan shekarun nan, an sami irin wanann takun saka a jihohi irin Kano da Sokoto da Adamawa da kuma Katsina dukkaninsu a sassan Arewacin Najeriyar, inda masana tarihi da al’adu ke kallon al’amarin a matsayin barazana ga tsarin Sarautar mai dogon tarihi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Informations
- Émission
- Chaîne
- FréquenceDeux fois par semaine
- Publiée11 février 2025 à 11:01 UTC
- Durée9 min
- ClassificationTous publics