154 episodes

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

Daga Laraba Aminiya

    • News

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

    Dalilin Da Za A Hana ’Yan Ƙasa Da Shekara 18 Shiga Jami’a

    Dalilin Da Za A Hana ’Yan Ƙasa Da Shekara 18 Shiga Jami’a

    Idan aka zagaya jami’o’i ana samun dalibai da dama wadanda ba su wuce shekara 15 ba a aji. A yanzu zamani ya sauya, abin ya zama Ruwan dare.

    Mai yiwuwa a lokacin da kuke makarantar firamare ko sakandare kun hadu da wadanda aka yiwa tsallaken aji, wato a bai wa dan aji 4 damar rubuta jarabawar kammala firamare ko kuma dan SS2 damar rubuta WAEC ya wuce jami’a

    Wannan ne ya sa gwamnatin tarayya ta ce za a tabbatar da dokar hana duk wanda bai kai shekara 18 ba zuwa matakin gaba da sakandare. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi duba a kan wannan lamari. 

    • 23 min
    Muna Rayuwa A Cikin Ƙunci - Ma’aikatan Najeriya

    Muna Rayuwa A Cikin Ƙunci - Ma’aikatan Najeriya

    Yau ce ranar 1 ga watan Mayu da aka ware a Najeriya da wasu sassan duniya domin jinjina ga rawar da ma’aikata ke takawa wajen ci gaban kasa. 

    Sai dai yayin da 'yan Najeriya da dama ke kuka da halin da aka shiga na ƙuncin rayuwa, ma'aikata na kan gaba wajen bayyana yadda suka ce suna tagayyara kuma aikin ba riba ta wani ɓangaren.
     
    Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba yadda rayuwar ma'aikata a Najeriya ke kasancewa da sauyin da ake fatan samu.

    • 25 min
    Me Ya Sa Kamfanonin Lantarki Suke Fifita ‘Yan ‘Band A’?

    Me Ya Sa Kamfanonin Lantarki Suke Fifita ‘Yan ‘Band A’?

    Bayan komawa tsarin rukuni daban-daban na bayar da wutar lantarki Idan kamfanoni na neman afuwa to yawancin ga ‘yan rukunin farko ne.

    Wasu na ji a ransu kamar su ba kwastomomi bane ga kamfanonin domin kulawar da ake ba su ta nuna ba a tare da su.

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba abin da ya sa hankalin kamfanonin wutar lantarki ya karkata wani fanni.

    • 25 min
    Yadda Sabbin Ma'aurata Ke Morewa A Ramadan

    Yadda Sabbin Ma'aurata Ke Morewa A Ramadan

    A watan Ramadan sabbin ma'aurata na alfahari da azuminsu na farko a gidan aure.

    Shin mene ne abin da yake kayatar da gidan aure musamman a wannan lokaci na Ramadan? Ya ya kamata ma'aurata su kasance?

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna yadda ma'aurata ke samun tabarruki da falala a yanayinsu na farko.

    • 22 min
    Abubuwan Da Ba A So Mai I'itikafi Ya Aikata

    Abubuwan Da Ba A So Mai I'itikafi Ya Aikata

    I’itikafi  sunna ce mai karfi a wannan lokaci, kuma jama’a masu sukunin shiga na kwashe kwanaki kusan goma a masallaci wajen ibada.
    To amma me ya kamata ku sani gameda shiga itikafi kuma wadanne abubuwa ake son mutum ya kiyaye a lokacin?

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba matakan yin i'itikafi da abubuwan da ya kamata ku sani gameda hakan.

    • 23 min
    Abin Da Ake Yi A Goman Tsakiyar Ramadan A Addini Da Al'ada

    Abin Da Ake Yi A Goman Tsakiyar Ramadan A Addini Da Al'ada

    A yayin da ake shiga goman tsakiya na watan Ramadan, malamai na kira ga al’umma da su dage wajen ibadu domin samun dacewa.
    A al’adance a wannan goma ta tsakiya akwai wasu al’adu musamman na tashe da kuma kirarin goma ta wuya bayan ta marmari.

    Shirin Daga Laraba ya yi tsokaci ne a kan wasu abubuwa da da ake yi a goman tsakiyar Ramadan a addinance da al'adance.

    • 29 min

Top Podcasts In News

بودكاست أريـــكة
Ghmza غمزة
الفجر
ثمانية/thmanyah
لقاء خاص مع رغد صدام حسين
alarabiya podcast العربية بودكاست
Forum ‐ La 1ère
RTS - Radio Télévision Suisse
The World in Brief from The Economist
The Economist
Lounge Talk
Lounge Talk