Ilimi Hasken Rayuwa RFI Hausa
-
- Education
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.
-
Tasirin sabuwar hanyar koyarwa a duniya
A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan sabuwar hanyar koyarwa, da kuma tasirin da ta ke da shi a harkar ilimi a faɗin duniya, wato Innovative Teaching Method a turance.
-
Yadda jaddawalin karatun Najeriya ke haifar ga koma-baya a Fannin Ilimin Kasar
A wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne a kan yadda tsarin jaddawalin karatun Najeriya ke haifar da koma-baya a fannin ilimin kasar.
-
Ban-bancin da ke da shi wajen karatun Ilimin kimiyya da fasaha a kasashen Duniya
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako, ya yi duba ne a kan tsarin ilimin kimiyya da fasaha tsantsa hadi da lissafi, wato STEM Education a turance. Mafi yawancin kasashen Duniya da suka ci gaba, na bawa wannan tsari na Ilimin Kimiyya da fasaha tsantsa hadi da Lissafi fifiko a makarantunsu, la’akhari da yadda kimiyya da fasaha a wannan zamani suka zama ginshinkin ci gaba a sararin wannan duniyar.
-
Jami'ar Umaru Musa ta yaye sama da dalibai dubu goma a wannan shekarar
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan yadda ake ci gaba da samun ci gaba a bangaren daliban da ke zuwa makaranta a yankin Arewacin Najeriya. Jami'ar Umaru Musa 'Yar Adu'a da ke jihar Katsina ta samu nasarar yaye sama da dalibai dubu 10 a wannan shekarar.
-
Yadda Jami'o'in Najeriya suka fara mayar da hankali kan karatun koyon sana'a
Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan yadda aka fara mayar dahankali a kan karatun koyon sana'a a Kwalejoji da Jami'o'i a Najeriya.
Kuna iya Latsa alamar sauti domin sauraron shirin... -
Yadda Dalibai ke bada gudunmawa wajen sarrafa sinadaran da basa gurbata muhalli
Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya duba yadda Dalibai a kasashen da suka ci gaba ke bayar da gudunmawa wajen sarrafa sinadarin "Hydrogene" da baya gurbata muhalli sosai, ta fuska kere-kere da nufin inganta iskar da ake shaka, bisa tallafin gwamnatocin kasashensu.