Lafiya Jari ce RFI Hausa
-
- Science
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.
-
Halin da ake ciki a yaki da cutar yunwa tsakanin kananan Yara a Jamhuriyar Nijar
A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya yi duba ne a kan halin da ake ciki a yaki da cutar Tamuwa tsakanin kananan Yara a Jamhuriyar Nijar.
-
Bayani a kan cutar ƙyanda da yadda za a kare yara daga kamuwa
A wannan makon shirin zai yi duba kan cutar kyanda ko kuma measles a turance, cutar da galibi akan ga bullarta a irin wannan lokaci da ake fama da matsanancin zafi musamman a yankunan kasashen yammacin Afrika Sahel.
-
Yadda matasa ke rungumar tsarin yin kaho a zamanance
Shirin lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan tsarin yin kaho a zamanance
-
Karancin ruwa na haddasa tarin cutuka ga al'ummar arewacin Kamaru
Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda al’ummar yankin arewacin kamaru ke fuskanta matsalar rashin tsaftatacce kuma wadataccen ruwan sha ba, wanda ke haddasa gagarumar matsala ga lafiyar mazauna yankunan, wannan shi ne maudu’in da shirin na wannan mako zai mayar da hankali akai.
-
Amfanin Azumi ga lafiyar jikin dan Adam
Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne game da alfanun Azumi ga lafiyar jikin dan Adam. Masana kiwon lafiyar dai na bayyana cewar Azumi na taimakawa wajen rage kaifin wasu cutuka a jikin dan adam.
-
Yadda ya kamata mai Azumi ya kula da kansa a lokacin zafi
Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne kan irin cutukan da ke karuwa a lokutan Azumi musamman yadda a wannan karon ake gudanar da ibadar a cikin yanayi na tsananin zafi, wanda masana ke ganin akwai wasu naukan cutukan da ka iya bijorowa. Masana kiwon lafiya dai sun gargadi masu dauke da wasu nau'ukan cutuka kan irin matakan da ya kamata su dauka don kula da lafiyarsu.