Al'adun Gargajiya RFI Hausa
-
- Noticias
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
-
Koken Jama'a a kan yadda hukumomi ke yi wa abubuwan tarihi rikon sakainar kashi
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi duba ne a kan yadda Jama'a ke koken game da rikon sakainar kashi da hukumomi ke yi wa abubuwan tarihi, kamar Makon jiya yau ma shirin ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya tattauna da shugaban kwamitin raya Al'adun Gargajiya na Majalisar dokokin Jihar, Hon. Sarki Aliyu Daneji.
Ku latsa alamar sauti don jin yadda shirin ya kasance.... -
Yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Kano da ke Najeriya
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya yi duba a kan yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Karofin Kofar Mata wadda ke da dogon Tarihi.
Shirin ya samu zarafin tattauna wa da Baballiya Hamisu, wanda shi ne mai magana da yawun Marinar ta Kofar Mata. -
Yadda tsadar rayuwa ke barzana ga Maroka da Sankira a Jamhuriyar Nijar
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya duba yadda jama'a a Maradi suka koma amfani da ruwan randa a maimakon kankara lokacin azumin watan Ramadana, saboda tsadar kankarar.
-
Yadda masarautar Hausawan Turai ke gudanar da ayyukanta
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Sarkin Hausan Turai Alhaji Surajo Jankado Labbo da ke kasar Faransa, inda Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi kan wasu batutuwa da suka shafi Hausawa.
-
Tasirin masu sarautar gargajiya wajen inganta tsaro a yankunansu
A sakamakon gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin Nigeria na 1976, aka tsame hannun sarakunan gargajiya a kasar cikin sha’anin kula da harkokin tsaro da harkokin shari’ah da kuma batun tara haraji a cikin al’ummarsu.Hakan ne ya sanya Sarakuna duk da kasancewarsu iyayen kasa, suka koma gefe inda suka zamo ‘yan kallo kan wadannan al’amura.
-
Yadda kananan kabilu suka samu wakilci a masarautar Katsinar Maradi
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Katsina Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, inda Sultan Ahmed Ali Zaki ya fitar da wani tsari na nada kananan kabilu a mukaman wakilan al’ummarsu, don kara dankon zumunci tsakanin kabilu sannan da raya al’adun gargajiya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.Baya ga Fulani da Bugaje da ke zama 'yan gida, Sultan ya nada wakilan Adarawa, Zabarmawa da Tubawa.