Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya duba yadda kasuwancin kifi a Najeriya ya ke neman ya gagari masu sana’ar saboda tsadar abincin da ake kiwon kifi da shi da farashin sa ya ƙaru, lamarin da ke barazana musamman ga ƙanana da matsakaitan ƴan kasuwa a fannin.
Farashin buhun abincin kifi ya tashi daga N18,000 a shekarar 2023 zuwa N36,000 a wannan shekarar, wanda ya nuna karuwar kashi 100 cikin 100 a fadin Najeriya.
Wannan al’amari ya yi kamari a yankin Neja Delta da suka yi kaurin suna a noman kifi.