
479 episodes

Najeriya a Yau Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim
-
- News
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
-
Abin Da Ya Sa Masu Zaman Waƙafi Ke Shafe Shekaru Ba Hukunci
Rayuwa ta kan sauya a duk lokacin da mutumin da ke zaman waƙafi a gidan kaso ya shafe dogon lokaci babu hukunci amma daga bisani aka sake shi.
Akwai dubban mutane da ke jiran yanke hukunci a kotuna da kuma waɗanda basu san makomar su ba.
To amma me ya sa ake samun wannan tsaiko? Abin da shirin Najeriya na yau ya duba kenan. -
Yadda ‘Yan Najeriya Ke Tafka Asara Saboda Wasa Da Lokaci
Lokaci daya ne daga cikin abubbuwan da ake wasa dasu masu matukar muhimmamnci a Najeriya. Wanda sakamakon hakan mutane na tafka asara.
Shin Mene ne abin da yasa ‘yan Najeriya ke wasa da lokaci?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya dubi wannan batu da idon basira. -
Shin Ko Akwai Lalaci Kan Yadda Wasu Mazan Kan Sakarwa Matan Su Ragamar Gida
Tun dauri a arewacin Naijeriya, Maza aka sani da rike da ragamar gida, ta hanyar fita a nemo abun da za a ciyar da iyali, yayin da mata ke lura da aikace-aikacen gida.
Wasu matan kan yi sana’o’i na gida da niyyar samun kudin kashewa da ba dole sai an tambayi maigida ba.
To a yanzu an shiga yanayin da wasu mazan ke sakarwa mata ragamar gida kacokan.
Shirin Naijeriya A Yau, ya yi duba ne kan wannan ta’ada ta wasu mazajen, da yadda matan ke fama wajen daukar nauyin gida. -
Matakan Da Za Ku Kare Lafiyar Ku A Lokacin Sanyi
Da zarar an shiga lokacin sanyi, a kan samu cututtuka da dama dake yawo saboda kaɗawar iska.
A gefe guda kuma akwai batun kula da lafiyar fata ga masu kaushin jiki da bushewar fata.
Shirin Najeriya a Yau ya duba matakan da ya kamata ku dauka wajen kare lafiyar ku a lokacin sanyi da hunturu. -
Shin Hukuncin Kotuna Kan Gwamnoni Ya Sauya Dimokariɗiyya?
Kotuna da dama sun yanke hukunci mabanbanta a kan kujerun gwamnoni, inda aka soke wasu da suke jam'iyyar adawa da ma jam'iya mai ci.
Ana ganin hakan kamar wani sauyi ne ga dimokraɗiyya wajen yanke hukunci ba sani ba sabo.
Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan ci gaban da aka samu ga dimokraɗiyya bayan hukunce-hukuncen kotuna kan kujerun gwamnoni. -
Yadda TikTok Ke Lalata Tarbiyyar Matasa
Raye-raye da tsalle-tsalle na rashin tarbiyya na ci gaba da samun karbuwa a kafar sada zumunta na zamani da ake wa lakabi da Tiktok. Ta yadda kusan babu irin rashin tarbiyyar da ba a bayyanawa a wannan kafa.
Shin wace irin illa wannan kafa take yi ga cigaban karatun matasan Najeriya?