Mu Zagaya Duniya RFI Hausa
-
- News
Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.
-
Gwamna Abba Yusuf ya mayar da Sarki Muhammadu Sunusi kan mukaminsa
Gwamnan Kano Abba Yusuf ya rattaba hannu a wata doka mai rusa ga baki daya masarautun Kano inda ya mayar da Sarki Muhammadu Sunusi kan mukaminsa.
Bashir Ibrahim Idris dangane da wannan mataki ya tattauna da Abdoulkarim Ibrahim da Nura Ado Suleiman a cikin shirin Duniyar mu a yau daga nan sashen hausa na Rfi. -
Bitar labaran mako: Bikin cika shekaru 17 da kafuwar Sashin Hausa na RFI
Daga cikin labarun da shirin na Muzagaya Duniya ya sake waiwaya akwai cikar Sashin Hausa na RFI shekaru 17 cif da kafuwa. Sai kuma matakin rushe sabbin masarautun da ya baiwa gwmna Abba Kabir Yusuf damar sake naɗa Sarki Muhammadu Sunusi na II a matsayin Sarkin Kano na 16.
-
Tattaunawa da Dr Kasim Garba Kurfi a shirin Duniyarmu a yau
Wannan shiri na Duniyarmu a yau zai dinga muhawara kan harkokin yau da kullum da ke dauke hankalin jama'a a duk ranar Asabar daga karfe 5.
Shirin na wannan mako ya karbi bakucin Dr Kasim Garba Kurfi mai sharhi kuma masanin tattalin arziki. -
Mutane 15 ne suka rasa mutu sanadiyar harin da matashi ya kai Masallaci a Kano
Daga cikin labarun da shirin wannan makon ya ƙunsa akwai harin da wani matashi a Kano ya kaiwa Masallaci ta hanyar cinna masa wuta, wadda zuwa lokacin gabatar da wannan shiri aka tabbatar da salwantar rayukan mutane 15 daga cikin akalla 30 da ke cikin Masalacin. Shirin na kuma ɗauke da tattauna wa da tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo, kan tuntubar junan da jiga-jigan jam’iyyun dawa suka fara yi a Najeriya, don kafa sabon ƙawancen da zai tunkari jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.
-
Shirin ya duba zaben Chadi da kuma shirin ECOWAS na kafar rundunar yaki da ta'addanci
Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman
-
Najeriya: Ƙarin albashi da gwamnati ta yi bai burge Ƙungiyar ƙwadago ba
Daga cikin batutuwan da shirin wannan lokaci ya waiwaya akwai, watsin da kungiyar kwadagon Najeriya ta yi da karin albashin ma’aikatan da gwamnatin kasar ta yi.
Sai kuma matakin Burkina faso na rufe karin kafafen yada labarai bisa rahoton da suka bayar na kisan fararen hula sama da 200 da sojoji suka yi.
A Kenya kuwa Ambaliyar ruwan ce ta lakume rayukan mutane da dama gami da raba wasu kusan dubu 200 da muhallansu.