Ilm Lectures Hausa

IlmQS

Islamic lectures in Hausa language from from world renowned scholars.

Episodes

  1. Fatawowin Rahama - Q&A 19-4-2026 - Prof. Sani

    21 APR

    Fatawowin Rahama - Q&A 19-4-2026 - Prof. Sani

    *Fatawoyin Rahma* Ranar Lahadi - 2/11/1447 - -19/4/2026 Tare da *Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON* ​ Hukuncin mutum ya bi limami mai ƙasaru sallah ba tare ya sani ba!​ Yaya ake wahayin hadithin ƙudusi ga Annabi ﷺ Hukuncin wanda ya ƙi biyan bashi alhali yana da halin biya?Idan abin hawan mutum ya lalace saboda ƙabarin tatsine ( speed breaker) , wa zai ɗauki alhaki?Shin mace mai haila ba za ta tsefe kai ba, ba za ta yanke akaifa ba?Mutane biyar da suka haɗu suka yi noma, za zu haɗu su fidda zakkar abin da suka samu?Ya hallata jami’in tsaro ya karɓi cin hanci domin yayi sadaƙa?Akwai uzurin da zai iya sa mutum ya rinƙa sallar Asuba a gida?Hukuncin wanda ba sa yin azkar bayan sallah nan take!Ya hallata a matse wajen kafa sahu a Sallah!Hukuncin wanda yake kwana a massallaci janaba ta same shi!Yaya ake shafa akan huffi?In mutum ya sanya safa da takalmi- akan wanne zai yi shafa?Mutum zai iya auren ‘yar da matar mahaifinsa ta haifa a wani gida?Akwai bambancin tsakanin hoton da aka zana da hannu da hoton aka ɗauka da camera?Dole wakilin ango ya sanar da ango dukkan sharuɗɗan da aka fada a wajen ɗaura aure?Hukuncin karbar bashi da sharaɗin za a ƙara kuɗi in an jinkirta biya?Hukuncin wanda ya ga jini a tufafinsa bayan yayi Sallah?Mafita ga mai yawan yin wasuwasi !Shin girmamawa ne mutum ya janye hannunsa in babba da ya miƙo masa hannu don musafaha!Ya hallata a aika gaisuwa ko ta’aziya ta hanyar rubuta maimakon yin magana!In mutum yayi sujjada sai ya manta sujjada ta ɗaya ce ko ta biyu, yaya zai yi?In mutum ya kama matarsa ta na waya da wani, mai ya kamata yayi? Yaya direba zai yi kaffara in mutane sun mutu a motar da yake tuƙawa?Haƙƙin wanda yake aiki a ƙarƙashin mutum!In mutum yayi sallar farilla da mutum ɗaya, zai iya sake wata in wasu mutane da yawa suka zo?Ya hallata musulmi ya sa hoton Kirsimas a shafinsa na sada zumunta!Hukuncin limami mai kusakurai karatun Fatiha!​ Hukuncin masu ɗaukar kayan da ake ba su a jirgin sama, kamar bargo da sauransu!Akwai zakka a waken suya da gyɗa?Ya hallata Da yayi amfani da layun da mahaifinsa ya bar masa!

    51 min

About

Islamic lectures in Hausa language from from world renowned scholars.