
97 episodes

Daga Laraba Aminiya
-
- News
-
-
5.0 • 1 Rating
-
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
-
Matakan Samun Nasara A Watan Ramadan
Ana sa ran a tashi da Azumin watan Ramadan mai albarka ranar Alhamis idan Allah ya yarda.
Shin kun san matakan samun nasara a cikin ibadar wannan wata?
Shirin Daga Laraba na wannan karo ya tattaro bayanai da shawarwari na alheri game da yadda za a rabauta da alheran da ke cikin watan azumin Ramadan. -
Hakikanin Abin Da Ya Sa Aka Ki Sakin Naira
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya leka banki da kasuwa kuma ya gano yadda jama’a ke fama da rashin kudi, ga shi kuma wasu ’yan kasuwa sam ba sa karbar tsohuwar Naira, sai sabuwa ko taransfa.
Ko yaushe za’a sakar wa ’yan Najeriya Naira?
Saurari Daga Laraba domin jin amsar wannan tambaya, dama wadansu masu alaka.
Za ku so karanta wadannan -
Wane Ne Bola Ahmed Tinubu? Bayani Daga Dattawan Legas
Shirin Daga Laraba na wannan karo ya yi wasu tambayoyi masu kalubale ga shugaban kasar Najeriya mai jiran gado game da lafiyarsa, da kuma kaifin basirarsa.
Shin Bola Ahmed Tinubu zai iya tafiyar da harkokin mulkin Najeriya fiye da Muhamadu Buhari?
Ku surari shirin Daga Laraba na wannan mako ku ji amsoshin duka tambayoyin namu. -
Ba-zatan da Zaben 2023 Ya Zo Da shi
Ku biyo shirin Daga Laraba na wannan karo ku ji yadda sakamakon zaben shugaban kasa da ’yan majalisun tarayya na shekarar 2023 ya zo da sabon salon da watakila ba a taba ganin irinsa a wannan zamanin ba.
A cikin shirin, za ku ji yadda gwamnoni masu ci suka sha kasa a yunkurinsu na zuwa Majalisar Dattawa. -
Anya INEC Ta Shirya Wa Zaben 2023?
Ranar Asabar 25 ga Watan Fabrairun da muke ciki ne ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasa da ’yan majalisun tarayyar Najeriya.
Shin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta shirya gudanar da wannan gagarumin aiki?
Shirin Daga Laraba ya leka lungu da sako a Najeriya domin sanin matakin shirin hukumar zaben da kai. -
Wa Zai Lashe Zaben Shugaban Najeriya?
Nan da kwana tara ’yan Najeriya za su zabi sabon shugaban da zai mulke su na tsawon shekaru hudu idan Allah ya yarda.
Bisa la’akari da yadda yakin neman zabe ke gudana, wane ne cikin ’yan takarar ke da alamun nasara a zaben na mako mai zuwa?
Shirin Daga Laraba ya tattauna da kwamitin yakin neman zaben manyan ’yan takarar da ake sa ran daya daga cikinsu zai zamaz zababben shugaban kasar Najeriya, inda kowannensu ya bayyana yadda yake kallon nasara da kuma kalubalen da ke gabansu. A yi sauraro lafiya.