Mu Zagaya Duniya

RFI Hausa

Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.

  1. Jun 27

    Ana ci gaba da laluben dubban mutanen da suka ɓata a girgizar kasa a Venezuela

    Shirin na wannan mako zai soma ne daga Venezuela inda a yammacin ranar laraba girgiza ƙasa mai karfin maki 7 a ma’aunin celcius ta afkawa arewa maso yammacin ƙasar abin da ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali da alhini sakamakon rasa rayuka da dukiyoyi. Alkaluman hukumomi sun ce sama da mutum 900 ne suka rasayukansu kawo yanzu yayin da sama da 4,000 suka jikkata bayaga sama da 50,000 da suka yi ɓatan dabo. Tuni dai Ƙasashe suka fara aike da saƙonni  jaje baya ga jami’an agaji don taimakawa a aikin laluben mutanen da girgizar ƙasa ta birne da kuma waɗanda ke cikin mawuyacin hali. A nahiyar Turai kuwa matsanancin zafi ya tilasta dakatar da harakokin yau da kullum a ƙasashe da dama. A wasu birane zafin ya kusa kai maki 40 a ma’aunin Celsuis abin da ya tilsatawa mahukunta fitar da gargaɗi da dakatar da  muhimman harakokin yau da kullum. A Faransa, an rufe ɗaruruwan makarantu a ranar Litinin yayin da aka rage lokacin tashin wasu dubbai. A wani labarin kuma, ranar Alhamis da ta gabata al’ummar musulmi mabiya ɗarikar Shi’a a duniya suka gudanar da juyayin tunawa da kisan jikan Annabi Muhammad SAW, da aka yi a garin Karbala na ƙasar Iraqi ta yanzu, kwanakin da ke yiwa laƙabi da Tasu’a da Ashura. A ƙasar Iran wadda itace cibiyar mabiya Shi’a a duniya an gudanar da bikin na wannan rana a cikin yaƙi da kuma rashin jagoran addinin ƙasar Ayatoullah Ali Khamna’ei, wanda ke jagorantar ranakun a kowacce shekara. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Oumarou Sani.

    21 min
  2. Jun 13

    Shirin ya fara da yadda aka buɗe bikin gasar cin kofin duniya a ƙasar Mexico

    Ranar Alhamis 11 ga wannan watan  aka yi  bikin buɗe gasar cin kofin duniya karo na 23, gasar da itace karo na farko da ƙasashe 3, Amurka da Canada da kuma Mexico su ka karbi baƙunci, sai dai kuma an gudanar da zanga-zanga a wasu sassa na birnin ƙasar. Ƙasashe 48 ne ke fafata domin samun zakaran bana kuma yan wasa 1,248 da alkalan wasa 52 za su jagoranci wasanni 104 da za'a kwashe kwanaki 39 ana yi. A cikin shirin akwai labarin, shugaban Amurka Donald Trump, da ya ce ya soke shirinsa na kai munanan hare-haren da ya shirya yi a Iran, sakamakon wata tattaunawar da yace ya yi da wasu ƙusosshin gwamnatin ƙasar, Ikrarin da ya zuwa yanzu hukumomin ƙasar basu ce komai akai ba. Haka zalika, Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da dokar kafa ƴansandan jihohi da gagarumar rinjaye, matakin da zai bai wa gwamnatocin jihohi damar kafa rundunar da za ta taimaka wajen magance matsalolin tsaron da suka addabi ƙasar. A Jamhuriyar Nijar gwamnati ce ta rattaɓa hannu a kan dokar haramta auran jinsi ko kuma mu’amalar jinsi guda wanda ta tanadi hukuncin ɗaurin da ka iya kai wa shekaru 20 a kan duk wanda aka samu da laifin yin haka. A wani abu da ba’a saba gani ba, Kungiyar mayaƙan JNIM mai alaƙa da Al Qaeda reshen Mali ta yi tayin bayar da tukwicin miliyoyin Yuro ga duk wanda ya ba ta bayanai kan inda shugaban kasar Assimi Goita  da manyan jami'an sojinsa suke, a yayin da ta bayyana gwamnatin a matsayin haramtacciyar. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin, tare da Oumarou Sani.

    20 min

About

Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.

More From RFI Hausa

You Might Also Like