Kasuwanci

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

  1. JAN 28

    Yadda aka ƙulla yarjejeniyar kasuwanci mafi girma a duniya tsakanin India da EU

    Yau shirin ya mayar da hankali ne dangane gagarumar yarjejeniyar cinikayya mafi girma da ba’a taba ganin irinta ba, da aka cimma tsakanin ƙungiyar Tarayyar Turain ƙasar India. Yarjejeniyar da aka cimma yayin ziyarar da shugabannin Turai suka kai New Delhi na ƙasar India, za ta bada damar kasuwanci mara shinge tsakanin ƙasashe mambobin EU 27 da kuma ƙasar da ta fi yawan jama'a a duniya, waɗanda suka kaɗai suka mamaye kusan kashi 25% na jimillar hada-hadar kasuwancin cikin gida na duniya da kuma cinkayyar mutane biliyan biyu. Domin ko a shekarar 2024 kaɗai, an yi cinikin sama da Euro biliyan 120 a tsakanin ɓangarorin biyu. Masu sharhi na ganin cewa kalaman wannan yarjejeniya da ɓangarorin biyu suka cimma, alaƙa da manufofin Shugaban Amurka, Donald Trump, musamman duba da yadda Tarayyar Turai ke ƙoƙarin faɗaɗa abokan hulɗar kasuwancinta, ba tare da dogaro da Amurka kaɗai ba. Yarjejeniyar dai na nufin cewa daga yanzu, India za ta soke ko kuma zaftare haraji kan hajoji da dama da take shigarwa yankin Turai, da suka haɗa da motoci daga kaso 110% zuwa 10% kachal, matakin da zai shafi kayan abinci da barasa da tufafi da kayan ado da dai sauransu. An dai ƙulla yarjejeniyar ce a daidai lokacin da mafi yawan ƙasashen duniya ke takun-saka da Amurka sakamakon haraji babu ƙaƙƙautawa da Donald Trump ke amfani da shi don tursasawa abokan hulɗa. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

    10 min

About

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

More From RFI Hausa