Hausa Fatwa

IlmQS

Islamic lectures in Hausa language from from world renowned scholars.

  1. 10 Sept

    Fatawowin Rahama: Q&A 30-08-2026 - Prof. Sani R/Lemo

    Fatawowin Rahma Ranar Lahadi 17/3/1448 - 30/8/2026 Tambayoyi tare da Amsoshi tare da *Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON* 1. Wacce hanya mutum zai bi ya zama ɗalibin ilimin hadisi! 2. Wanda ya samu raka’a ta ƙarshe a Sallar Magriba, yaya zai kammala Sallarsa? 3. Hukuncin wanda ya rikice ya kasa tuna raka’a nawa yayi? 4. Lamarin wadda in za ta yi Sallah sai ta ji kamar wani abu zai faɗo mata? 5. Hukuncin mutuwa a wurare masu falala? 6. Laifin wanda ya taimaka wajen zubar da ciki dai dai yake da wanda ya kashe wanda aka haifa? 7. Mutum zai iya yafewa wanda yake bi bashi da ya mutu ba sai ya fadawa iyalan mamacin ba? 8. Ya hallata mutum yayi sadaqa ga iyayensa da suka rasu! 9. Yaya mutum zai sa riba ga kayan da yake sayarwa! 10. Idan aka gina coci a Fili ba tare da izininsa mai filin ba, yaya magada za su yi? 11. Sallar ƙasaru ga matafiyi! 12. In mutum zai cutu a hanyar sa ta zuwa massallaci, zai iya Sallah a gida sannan kuma ya samu ladan wanda ya je massallaci? 13. Mamu zai iya ƙin bin liman da ya hada Sallah in mamun yana ganin sharuɗɗan haɗa sallolin ba su cika ba? 14. Yaya hukuncin Tela da yake aiki a shagon da wutar lantarki da aka janyo zuwa shagon ta sata ce? 15. Akwai addu’ar rufe gida ko daki? 16. Ana iya tofi da shafawa yaro yayin yi masa addu’a safe da yamma? 17. Mace za ita iya Sallah da zani da hijabi da ya rufe jikinta, ko da bata da riga? 18.kashin kaji najasa ne? 19. Hukuncin mutumin da aka bawa bashi da riba amma yake musun haka? 20. Hukuncin Wucewa gaban mamu ta kofar da aka bar ta a bude domin wucewar mutane! 21. Mace za ta iya Sujjadar Tilawa ba tare da hijabi ba? 22. Mutum zai iya azumin domin ya samu lada sannan ya rage kiba? 23. Mutumin da yayi alwala, yayi Azkar din bacci sannan ya sadu da iyalansa, sai ya sake Azkar? 24. Mutumin da yake Sallar dare, an ina ya kamata yayi addu’oinsa? 25. Yaya ya kamata musulmi ya gaishe da manya? 26. Akwai hadisin da ya ce za a fara sahu daga tsakiyar sahu?

    Fatawowin Rahama: Q&A 30-08-2026 - Prof. Sani R/Lemo
  2. 19 Aug

    Fatawowin Rahama: Q&A 9-8-2026 - Prof. Sani R/Lemo

    *Fatawoyin Rahma* Ranar Lahadi 25/2/1448 - 9/8/2026 Tambayoyi da Amsoshi tare da *Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON* 1. Hukuncin Dillanci! 2. Mutumin da yake so wata, ita ma take sonsa, amma iyayensa ba sa son su tare; yaya zai yi? 3. Hukuncin wanda ya ci abinci yana azumi da mantuwa! 4. Hukuncin yin kyauta ga ma’akacin Immigration da yayi aikin yin passport ga mutumin da ya masa kyauta! 5. Hukuncin rage shekaru don a daɗe a na aiki? 6. Hukuncin kiwon dabbobi domin siyarwa Kiristoci lokacin bukkunansu! 7. Ya hallata mutum ya bibiyi ma’aikatu domin bankaɗo cin hancin da rashawa? 8. Hukuncin ta da iƙama bayan Kiran sallah-ba tare da tazara ba. 9. Yaya hukuncin tube mace tumbur a mata tiyata! 10. Hukuncin yara da ba sa turawa mahaifinsu kuɗi saboda ya na da kuɗi kuma mahaifiyar su ta umurce su da ka da su ta ra masa! 11. Ta yaya mutum zai bambance jarabawar da Allah ya masa saboda laifinsa da kuma jarabawar da Allah ya yi masa domin daukakar darajarsa! 12. Dole ne mutum ya san ma’anar adduar da ya ke yi? 13. Yaya ake yin Istikhara? 14. Za a yi salatin Annabi ﷺ a sallar nafila? 15. Wanda ya mutu ta hanyar nitsewa a ruwa ko gobara, za a masa wanka? 16. Shawara ga mai fama da matsanancin wasuwasi? 17. Hukuncin wanda yayi ƙarya akan halayyar wani mutum! 18. Yaushe ake “ as-sallatu khairul minannaum”? 19. Falalar Limanci? 20. Ana yin azumin kaffara ga wanda ba musulmi ba? 21. Hukuncin Jami’an tsaron da suke hana wanda aka tsare yin sallah!

    Fatawowin Rahama: Q&A 9-8-2026 - Prof. Sani R/Lemo
  3. 21 Jul

    Fatawowin Rahama: Q&A 5-07-2026 - Prof. Sani R/lemo

    Fatawoyin Rahma Ranar Lahadi 20 /1/1448 - 5/7/2026 Tambayoyi da Amsoshi tare da _Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON_ ​ Mutumin da aka ɗauke shi aiki da sharaɗin zai zo tun ƙarfe takwas na safe zuwa ƙarfe biyar na yamma; zai iya tashi kafin ƙarfe biyar in ya gama aiki da aka sa shi? ​ ⁠Shin wanda ya je wajen boka ba da sanin boka bane, hukuncin ko yayi sallah na kwana 40 ba za a karba ba zai hau kanshi? ​ Wanda yayi Sallar Asuba a masallaci sai ya koma gida yayi zikiri har rana ta fito sannan yayi sallah raka’a biyu; zai samu ladan wanda yayi Hajji da Umra? ​ Mutum zai iya karbar Kwangilar aikin coci? ​ Mutumin da yayi zina ya tuba, Allah zai karbi tubansa ko da ba a masa haddi ba? ​ Hukuncin wanda ya ba da shaidar karatunsa ga wani ya yi amfani da takardun domin ya samu aiki da takardun! ​ Ya hallata mutum yayi addu’a da ayar Al-Kur’ani a cikin Sujjada? ​ Hukuncin sauraron waƙa! ​ Wanda suka sha ruwa saboda ladan ya kira Sallah kafin lokaci da kuskure; shin za su rama azumin? ​ Hukuncin mai gıda, mawadaci da ya dauki yaro aiki amma ba ya biyansa yadda ya dace! ​ Mutumin da yake shugabantar ma’aikata, zai iya ba kansa kwangila? ​ Mutumin da aka yi yarjejeniya da shi ba zai yi wani aiki ba, alhali albashin da ake ba shi ba ya isan sa; zai iya karya wannan yarjejinar ya nemi wani aiki! ​ Yaya hukuncin albashin wanda ya canza shekarun haihuwarsa yayin daukarsa aiki? ​ Mutum zai iya ware lokaci yayi karatun Al-Kur’ani domin ladan ya je ga mahaifarsa? ​ In mutum ya siffanta matarsa da wata dabba; hakan ma zihari ne? ​ Mutum zai iya amfanin da kudin ruwan Banki? ​ Yaya hallata mutum ya cigaba da zama da matarsa bayan ya kamata har sau uku tana tattaunawa da maza? ​ Ya hallata mutum ya bawa malaminsa Zakka? ​ Marar lafiya da ake bi azumi har na shekara uku, ya fara rama sai ciwon ya dawo, yaya zai yi?

    Fatawowin Rahama: Q&A 5-07-2026 - Prof. Sani R/lemo
  4. 12 Jul

    Fatawowin Rahama: KISHIN ƘASA - Prof. Sani R/lemo

    *Fatawoyin Rahma* Ranar Asabar 19/1/1448 - 4/7/2026 Tare da *Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON* Shimfida : *Kishin Kasa!* Tambayoyi da Amsoshi: 1. Mace za ta iya yin ɗawafi ko sa’ayi da niƙabi? Menene hukuncin kitso da yin lalle yayin Hajji ko Umra? 2. In mace ta yi allurar tsarin iyali sannan jini yana rikice mata; yaya za ta gudanar da sallarta? 3. Idan mai gyaran mota yana samun rangwame akan kuɗin abubuwan da za a gyra mota da ya karɓa daga wajen waɗanda suka kawo masa aikin gyran mota; ya hallata yayi amfani da rangwame da ya samu? 4. Hukuncin kuɗin ruwa da Bankuna suke bayarwa? Mutum zai iya aikin alhairi da kuɗin ruwa? 5. Yaya wanda yake da kaddarori daban daban zai fitar da Zakka? 6. Shin bandaki a ɗaki yana jawo aljanu? 7. Ya hallata mutum yayi mummunar addu’a ga azzalumin shugaba? 8. Yaya hukuncin fara alwala da Bismillah! 9. Hukuncin wanda ya karanta Fatiha a Sallah ba tare da Bismillah! 10. Menene hukuncin mace da ta gama jinin al’ada ta yi wanka, sai daga baya jini ya dawo, yaya za ta yi? 11. Wace addu’a ake yiwa yara Safiya da Maraice don neman kariya? 12. Hukuncin amfani da sunan Mahaifin da ba naka ba *Domin Samun karatukan Malam ku bibiyi wannan shafuka:* Facebook: https://www.facebook.com/Drmuhdsaniumarmusa/ Twitter: https://twitter.com/DrMSaniR_Lemo Instagram: https://www.instagram.com/drmsanirijiyarlemo Telegram:https://t.me/drmsaniumar YouTube: https://youtube.com/channel/UCa9nK0j55mr9PPhv4k3Wmbw Website:http://www.drmsanirijiyarlemo.net *Domin Sauke Manhajar Tafsirin Alƙur'ani :* Android: https://play.google.com/store/apps/details?id=online.smartech.basayir.hausa Apple : https://apps.apple.com/us/app/maanoni-da-shiriyar-alqurani/id6480479512 https://sanachannelstv.wuiltweb.com/ *Domin Tallafa wa Asusun Sautul Haq:* Account Number: 0010885007 Taj Bank Account Name: AL - IMAMUL BUKHARI CENTER FOR RESEARCH AND TRAN

    Fatawowin Rahama: KISHIN ƘASA - Prof. Sani R/lemo

About

Islamic lectures in Hausa language from from world renowned scholars.

You Might Also Like